Skip to main content
Logo image

Section 1.1

Mahimman abun koya
  • Dalibai za su fahimci cewa kirkira ya ƙunshi jerin umarni
  • Dalibai za su fahimci mai ma kirkiri ya ke yi
  • Dalibai za su fahimci aikin ma kirkiri
  • Dalibai za su fahimci sashen Masarrafar Bayanai, na’urori masu shigar da ko fitar da bayanai, RAM, Ma’aji na biyu - (sassan kwamfuta) muhimman sassan kwamfuta
Menene kirkira? Sannan ta yaya zan iya fara kirkira? Ina dai tsammanin ka kasance a wannan wajen ne domin wannan manufa. Ko koma ka na su ka tuna wasu abubuwa game da sha’anin kirkirar manhaja da ka taba karantawa a baya. Koma dai yayane, wannnan littafin zai kasance maka wani haske ne da zai kasance mafarin sanin wannan harkan na kirkira. Saboda haka, ina tsammanin a karshen wannan littafin zaka fahimce abubuwa da dama akan wannan fanni na kirkirar manhaja, sannnan ina tsammanin harma za ka samu damar iya kirkirar naka karamun manhajar.

Exercises Exercises

1.

    Ka shirya?
  • Na fahimta abubuwan baya
  • Write feedback
  • A’a (change)
  • write feedback
Wannan littafin zai haskakawa dalibai duniyar kirkire-kirkire mai ban al’ajabi. To amma yanzu bari in fara da amsa wancen tambaya da aka yi dazu, wato menene kirkira? Menene kirkira? Kirkira wani hanyace na samar da wasu sinkin umarni da na’urar mai ƙwaƙwalwa (kwamfuta) zai iya aiwatar da. Taron umarni da kamfuta za ta iya aiwatar da, ake kira ‘program’ wato ayyuka. Line break Mutumin da yake rubuta wannan ‘program’ (aiki) shi ake kira da ‘programmer’ wato makirkiri. Wata kalmar da ake kiran (program) aiki itace ‘software’ wato manhaja. Sannan ana iya kiran kalmar ‘programmer’ wato makirkiri da makirkirin manhaja wato ‘software developer’. To amma dai duk wannan ba shine abin tambaya a wajen mutumin da yake sabo a wannan babin ba. Tambayar dalibe anan ba zai wuce yace ta yaya na’urar komfiwta ke iya daukar wadannan jerin umarnin da makirkirn ya rubutasu sannan ya sarrafasu harma ya aiwatar da ayyuka da dama da aka sanya da yayi a cikin wannan jerin umarnin ba. Wannan dama sauran amsar wasu tambayoyin da ba a yisu anan ba zasu zo a nan gaba kadan a wannan littafin in Allah ya yarda.
culturally relevant examples

Exercises Exercises

1.

    Menene aikin makirkiri?
  • Rubuta umarni da kwamfuta za ta aiwatar da
  • Write feedback
  • Hada kwamfuta
  • write feedback
  • gaya wa mutane abin da za su yi
  • write feedback
You have attempted of activities on this page.